Sabuwar dangantaka a tsakanin Nahiyar Afrika da Turai | Labarai | DW | 08.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar dangantaka a tsakanin Nahiyar Afrika da Turai

A wani lokaci ne a nan gaba za a fara taron ƙolin hadin gwiwa a tsakanin ƙasashen Turai da Afrika. Za a gudanar da taron a tsakanin Nahiyoyin biyu ne, a birnin Lisbon na ƙasar Purtugal. Taron a cewar rahotanni na a matsayin irinsa na farko ne, a tsawon shekaru bakwai da su ka gabata. Bayanai sun shaidar da cewa taron zai mayar da hankaline wajen cimma haɗin kai, a fannonin tattalin arziƙi da cinikayya da kuma muhalli. Shugaba Mugabe na Zimbabwe da ake ganin ba zai halarci taron ba, tuni a jiya ya isa Lisbon don halartar wannan taro. Faraministan Biritaniya Mr Godon Brown ya yi kurarin ƙauracewa taron, bisa kasancewar shugaba Robert Mugabe a taron ƙolin. Biritaniya dai na zargin Mugabe da mulkin danniya da kama karya ne a ƙasar,wanda hakan ya kai ga take haƙƙoƙin miliyoyin ´Yan ƙasar.