Sabuwar barazana a Naija Delta | Labarai | DW | 20.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar barazana a Naija Delta

Kungiyar yan gani kashe ni da suke rike da turawa 4 da suka sace a yankin Naija Delta a Najeriya, sun sake yin barazana a yau na ci gaba da kai hare hare a yankin.

Kungiyar da ta kira kanta mai kwato yancin jamaar yankin,wadda tashe tashen hankula da ta haddasa ya kara farashin mai mafi tsauri cikin watanni 4 a kasuwannin duniya,ta bukaci kanfanin mai na shelll daya biya dala biliyan daya da rabi a matsayin diyya ga jamaar yankin saboda gurbata muhallinsu.

Tace koda kuwa an biya wannan kudi bazata dakatar da haren haren ba akan sauran kanfanonin mai dake yankin.

Kungiyar ta kuma sabunta kiranta na a sako shugabannin yan kabilar Ijaw da ake tsare da su.