1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar allurar riga-kafin cutar AIDS

Mohammad Nasiru AwalFebruary 17, 2004
https://p.dw.com/p/Bvlo

Sunan wannan allura dai tgAAC09, wadda masana kimiyya ke fatan cewar zata kare dan Adam daga kamuwa da kwayoyin HIV mai haddasa cutar AIDS ko SIDA. A cikin zagaye na farko na gwajin wannan allura ana neman mutane kimanin 50, da zasu fito bisa radin kansu a kasar Belgium da kuma a nan Jamus don gwada karfi da ingancin allurar riga-kafin a kansu. Shugaban masana kimiyya da suka kirkiro allurar rigakafin ta AIDS Dr. Jan von Lunzen na asibitin Eppendorf dake birnin Hamburg ya ba da tabbacin cewa babu wani hadari da zai rutsa da wadanda zasu zama zakaran gwajin dafin allurar. O-Ton Lunzen:

"Babu wani hadari na kamuwa da cutar, domin kwayoyin cutar ´yan kadan ne muka yi amfani da su, kuma an rigaya an tabbatar da cewa allurar ba zata harbi kowa da wata cuta ba. Da farko abin da muke so mu tabbatar shine karfin maganin da kuma yadda dan Adam zai iya jure ma sa. Burin mu na gaba a wannan bincike shine mu gano yadda wasu halittu a cikin jinin dan Adam zasu karbi sabon maganin musamman don hana kamuwa da kwayoyin HIV."

Wannan sabuwar allurar riga-kafin dai zata ba da kariya daga kamuwa da nau´in kwayoyin Typ C na HIV. Wadannan kwayoyin dai su ne ke haddasa kamuwa da cutar HIV a duk duniya musamman a kasashen Afirka kudu da Sahara da kuma yankin kudu maso gabashin Asiya. A wadannan yankunan kashi biyu cikin uku na mutane sama da miliyan 40 da suka kamu da cutar AIDS a duniya, suke. Baya ga cewar sabuwar allurar riga-kafin an hada ta ne gaba daya da kwayoyin halitta, wani abin alfanu da ta fi sauran magungunan cutar shine ta na da ingancin gaske.

Allurar dai na iya sake farfado da wasu kwayoyin halittu na garkuwa dan Adam da suka yi rauni. Haka zalika wannan allurar sau daya ake yiwa mutum, saboda haka zata ba da gagarumar gudummawa a kasashe masu tasowa. Tabbacin da masanan kimiyyar suka bayar game da ingancin wannan allurar riga-kafin ya dogara ne akan nasarar da aka samu na gwajin ta akan birrai. Wannan allurar dai zata taimaka wajen magance yaduwar annobar cutar AIDS. Kuma kasancewar magungunar rage radin cutar na da tsadar gaske musamman ga kasashe masu karamin karfi, wannan allurar riga-kafin zata zama mai muhimmanci wajen magance matsalar AIDS. A dai halin da ake ciki mutane kimanin 600 ke kamuwa da cutar a ko-wace awa daya. Saboda haka da akwai bukatar daukar matakan gaggawa don magance wannan annoba. A cikin shekara mai zuwa ake sa ran samun sakamakon farko na gwajin sabuwar allurar, amma za´a dauki akalla shekaru biyar kafin a samar da ita ga kowa da kowa.