Sabon yunkurin diplomasiya na warware rikicin Isra´ila da Libanon | Labarai | DW | 22.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon yunkurin diplomasiya na warware rikicin Isra´ila da Libanon

A gobe lahadi idan Allah Ya kaimu sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice zata je yankin GTT inda zata gudanar da shawarwari akan rikicin Libanon da Isra´ila. Ta fadawa wani taron manema labarai a birnin Washington cewar zata kuma halarci wani taron kasa da kasa da Italiya zata karbin bakoncinsa ranar laraba a birnin Rom. Shi ma ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier a yau zai yake shirin zuwa kasar Masar kafin ya karasa zuwa Isra´ila inda zai gana da FM Ehud Olmert da ministar harkokin waje Zippi Livni da kuma ministan tsaro Amir Peretz. Zai kuma gana da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas. A shekara ta 2004 Steinmeier ya taka muhimmiyar rawa a musayar firsinoni da aka yi tsakanin Isra´ila da Hisbollah.