1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon shugaban Pilipin zai dawo da hukuncin kisa

Zababben shugaban Pilipin Rodrigo Duterte ya yi alkawarin zai dauki matakan da za su kawo karshen aikata laifuka ciki har da dawo da hukuncin kisa.

Zababben shugaban kasar Pilipin Rodrigo Duterte ya ce sai sake dawo da hukuncin kisa kamar yadda ya yi alkawari lokacin yakin neman zabe.

Duterte ya sha alwashin kawo karshen miyagun laifuka a wannan kasa da ke yankin kudancin Asiya. Ya ce za a sake dawo da hukauncin kan laifuka kamar safarar miyagun kwayoyi, da fyade, da kisa, da kuma fashi da makami.

Rodrigo Duterte tsohon magajin garin Davao na kudancin kasar ta Pilipin ya lashe zaben makon jiya da gagarumin rinjaye, inda ranar 30 ga watan gobe na Yuni zai dauki madafun ikon kasar.