Sabon shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza, Abdel Aziz Al Rantisi. | Siyasa | DW | 24.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon shugaban kungiyar Hamas a Zirin Gaza, Abdel Aziz Al Rantisi.

Abdel Aziz Al Rantisi

Abdel Aziz Al Rantisi

"Hade kawunan Falasdinawa tare da ci-gaba da boren Intifida shine babban buri na a nan gaba." Da wannan gejeren lafazin amma watakila mai muhimmanci, magajin tsohon shugaban kungiyar Hamas, marigayi Sheikh Ahmad Yassin, ya takaita abubuwan da ya ke burin cimma nan gaba. A jiya dai ne aka nada Abdul Aziz Al-Rantisi a mukamin sabon shugaban kungiyar Hamas a yankin Zirin Gaza. Wannan dai wani canji ne da zai sa komai ya kara ta´azzara. Har wa yau shugaban kungiyar kanta shine Khaled Mishal wanda ke zaune a birnin Beirut na kasar Lebanon, yayin da shi kuma Al-Rantisi zai jagoranci bangaren kungiyar a Zirin Gaza. Zirin Gaza dai shine babban sansanin Hamas kuma a nan ne ta fi yawan magoya baya. Ban da haka Al-Rantisi wani mutum ne da aka san shi da bayyana manufar sa ta tsattsauran ra´ayi a fili.

O-Ton Rantisi:

"Ba Sheikh Ahmed Yassin ka dai suka yiwa kisan gilla ba, manufar su ita ce su halaka mu baki daya. Shi yasa muna fadawa wadannan ´yan kisa kuma ´yan ta´adda cewa yanzu zamu shiga yaki da su gadan-gadan."

Ana iya tantance ma´anar wadannan kalaman daga wasu furuce-furuce da Al-Rantisi yayi. Domin a lokacin da yake tofa albarkacin bakinshi, bayan wani harin kunar bakin wake da wani dan Hamas ya kaiwa wata bas a birnin Kudus kuma ya halaka ´yan Isra´ila 18 kimanin shekaru biyu da suka wuce, sabon shugaban na Hamas cewa babu dan Isra´ila da ba shi da laifi domin sun mamaye yankunan Falasdinawa kana kuma suna yiwa kananan yara da fararen hular Falasdinu kisan gilla. Isra´ila na zargin shi da hannu a kusan dukkan hare-haren da Hamas ke kai mata. Da shi da marigayi Sheikh Yassin suka kafa kungiyar Hamas a cikin shekarar 1987. Al-Rantisi mai shekaru 56 da haihuwa kuma kwararren likitan yara, sananne ne a kasashen yamma, domin, saboda kwarewarsa a harshen ingilishi, ´yan jaridar kasashen yamma sun fi yin hira da shi. To sai dai tun bayan yunkurin kisan shi da Isra´ila ta yi a cikin shekarar da ta wuce, ba´a fai ganin shi a bainar jama´a ba. Kalaman da yayi game da hade kan Falasdinawa tare da ci-gaba da yiwa Isra´ila bore yayi daidai da ra´ayoyin kusan dukkan al´umar Falasdinu kamar yadda wani masanin siyasar Falasdinawa Farfesa Ali Al Jarbawi ya nunar:

"Bayan kisan gillan da aka yiwa Sheikh Yassin talakawa da dukkan kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya ke wani yunkuri da nufin hade kawunansu. Wato kenan za´a samu wani sabon yanayi na tuntubar juna tare da goyawa juna baya tsakanin kungiyar Hamas da sauran al´umar Falasdinu."

Shi ma Al-Rantisi ya nunar da haka a fili, inda ya nunar da cewa shi mai cudanya ne da talakawa don hade kawunansu tare da karfafa adawar da suke nunawa Isra´ila. Ita ma hukumar mulkin Falasdinawa ba zata so ta nisanta kanta da wannan sabon hadin kan ba, domin kamar yadda Isra´ila ta nunar ne, ba kawai shugabannin Hamas zata ci-gaba da yiwa kisan gilla ba, a´a hatta shi kanshi jagoran Faslasdinawa Yasser Arafat na cikin jerin mutanen da Isra´ila ke shirin halakawa nan gaba.

 • Kwanan wata 24.03.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvl7
 • Kwanan wata 24.03.2004
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvl7