1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon Shugaban Kasar Jamus Horst Köhler

May 24, 2004

Takaitaccen tarihin zababben shugaban kasar Jamus mai jiran gado Horst Köhler

https://p.dw.com/p/BvjM
Sabon shugaban kasar Jamus bayan kammala zabensa
Sabon shugaban kasar Jamus bayan kammala zabensaHoto: AP

Horst Köhler yana da shekaru 61 da haifuwa kuma kwararren masani ne a fannin kudi da tattalin arziki, wanda ya taba rike mukamin karamin minista a gwamnatin Helmut Kohl kuma yayi darektan asusun ba da lamuni na duniya IMF dake birnin Washington har ya zuwa lokacin da aka ba da shawarar gabatar da shi domin takarar mukamin shugaban kasar Jamus. Ba dai tare da wata rufa-rufa ba ya fito fili ya bayyana gaskiyar cewar ba ya da wata kakkarfar alaka da ‚yan siyasa a nan kasar ta Jamus. Bai taba shiga inuwar wata jam‘iyyar siyasa domin taka wata rawa ta a zo a gani ba. Amma fa a daya bangaren mutum ne da yayi fice a dangantakar kasa da kasa, kamar yadda aka ji daga bakinsa jim kadan bayan da aka nada shi takarar neman mukamin shugaban kasar, inda ya ci gaba da cewar:

Bayan aikina na tsawon shekaru hudu a Washington da kuma wasu shekaru biyu da na yi a Bankin Turai domin ayyukan sake ginawa da manufofin raya kasa a birnin London na samu wata cikakkiyar kafa ta saduwa da kuma cude-ni-in-cude-ka da mutane daga kowace kusurwa ta duniya. Hakan abu ne da ya taimaka mini wajen bin sassaucin ra’ayi da haba-haba da mutane. Ni kan dokata in sadu da mutum domin jin ta bakinsa. Wannan ba shakka abu ne da zai amfanar da kasa baki daya.

A karkashin wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Hitler da Stalin aka canza wa danginsa mazauni daga yankin Modabiya zuwa Skierbieszow da ya kasance karkashin mamayar kasar Poland a zamanin baya. A nan ne kuma aka haifi Köhler a shekarar 1943. Dangin nasa sun tsere daga wannan yankin sakamakon tuttudowar sojojin Rasha inda suka nemi mafaka a Ludwigsburg dake kusa da birnin Stuttgart. Bayan da ya kammala makarantar sakandare da kuma aikin sojan bauta wa kasa, jami’in ya nazarci kimiyyar tattalin arziki a jami’ar Tübingen sannan ya ci gaba da aiki a cibiyar binciken kimiyyar tattalin arziki ta jami’ar bayan samun digirinsa na likita. Ya kama aiki a ma’aikatar kudi ta Jamus a 1976. A 1981 tsofon gwamnan jihar Schleswig-Holstein Gerhard Stoltenberg ya nada shi kan mukamin maga-takarda a fadarsa dake Kiel, kuma bayan nadin Stoltenberg kan mukamin ministan kudi a gwamnatin Helmut Kohl sai ya nada shi darektan sashen kula da manufofin kudi na ma’aikatar. Ya zama karamin minista a ma’aikatar ta kudi ne a shekara ta 1990, inda ya rika share fage ga shugaban gwamnati Helmut Kohl domin halartar tarukan koli na tattalin arziki. A 1993 Köhler ya zama darektan gamayyar bakunan ajiya na Jamus kafin a nada shi shugabancin Bankin raya kasashen gabacin Turai a 1998. Shekaru biyu bayan haka ya zama darektan asusun ba da lamuni na IMF a birnin Washington, mukamin da ya rike har ya zuwa lokacin nadinsa domin takarar neman zama shugaban kasar Jamus.