sabon shugaban hukumar kwallon kafa na turai | Labarai | DW | 26.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

sabon shugaban hukumar kwallon kafa na turai

An zabi Mr Michael Platini a matsayin sabin shugaban hukumar gudanarwa na kungiyar kwallon kafa na turai,UEFA.Mai shekaru 51 da haihuwa ,kuma tsohon captain din tawagar yan wasan kasa na kasar Faransa ,Platini ya samu nasar akan abokin takararsa Lennart Johansson dan kasar Sweden,da kuriu 27 daya samu kana shi kuwa 23,a zaman taron daya gudana a birnin Dusseldorf dake yammacin Jamus.Mai shekaru 77 da haihuwa,Mr Johansson ya shugabanci hukumar a karonsa na farko a 1990.