1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban Benin ya yi rantsuwar kama aiki

Salissou BoukariApril 6, 2016

A wannan Laraba ce sabon shugaban kasar Benin Patrice Talon da aka zaba ka fiye da kashi 65 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada ya yi rantsuwar kama aiki a Porto-Novo.

https://p.dw.com/p/1IQHW
Westafrika Benin Unterstützer des Präsidentschaftskandidat Patrice Talon
Magoya bayan sabon shugaban kasar Benin Patrice Talon suna murnaHoto: Reuters/C. P. Tossou

An yi wannan biki ne dai a babban filin kollon kafa na Charles de Gaulle da ke Porto-Novo babban birnin kasar a gaban wakillan siyasa da shugabannin gargajiya da ma jami'an diflomasiyya masu wakiltar kasashen waje a kasar ta Benin, amma ba tare da halarta shugabannin wata kasa ba.

Jim kadan bayan rantsar da shi kuma bayan da ya yi wata tattaunawa ta sirri da Shugaban kasar mai barin gado Docta Thomas Boni Yayi. Sabon shugaban kasar ya isa a fadarsa ta Marina da ke birnin Cotonou cibiyar kasuwancin kasar, inda ya ziyarci jerin jami'an tsaro da suka zo domin karramashi.