1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon Salon zubi da tsarin Siyasa a Afrika Ta Kudu

Ibrahim SaniDecember 22, 2007
https://p.dw.com/p/Cf3G

Shugaba Thabo Mbeki na Afrika Ta Kudu ya ce dole ne doka tayi halinta, kan zargin cin hanci da rashawa da akewa Mr Jacob Zuma. Aiwatar da wannan mataki a cewar Mbeki, abune da zai taimaka wajen saisaita fage na harkokin siyasa a ƙasar. Kafafen yaɗa labarai sun rawaito Mr Zuma na cewa har yanzu babu wata tuntuɓa da akayi ma sa, dangane da zargin cin hanci da rashawa. Mr Mokotedi, dake zaman babban mai gabatar da ƙara a Afrika Ta Kudu ya ce har yanzu akwai sauran rina a kaba, dangane da zargin cin hanci da rashawa da akewa Mr Zuma. Jami´an ya tabbatar da cewa akwai gamsassun hujjoji, da za su haifar da gurfanar da Mr Zuma a gaban ƙuliya. Tuni dai magoya bayan Zuma su ka yi watsi da zarge-zargen da cewa siyasa ce kawai. A ranar talata ne Mr Zuma ya kayar da shugaba Thabo Mbeki, a zaɓen shugaban Jam´iyyar ANC da aka gudanar. Hakan dai na a matsayin sharar fage ne ga Mr Zuma, na zamowa shugaban ƙasar Afrika Ta Kudu a shekara ta 2009.