Sabon salon warware rikicin yankin gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 16.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon salon warware rikicin yankin gabas ta tsakiya

Sakatariyar harkokin wajen Amurka CR, tace nan gaba zata shirya tattaunawar sulhu a tsakanin ta da Faraministan Isreala, Mr Ehud Olmert da kuma takwaran sa na Palasdinawa Mahmud Abbas.

CR, wacce ta fadi hakan jim kadan bayan ganawar ta da Shugaba Hosni Mubarak na masar, tace tattaunawar a tsakanin shugabannin uku, zata mayar da hankali ne wajen samo bakin zaren warware rikicin yankin gabas ta tsakiya, musanmamma a tsakanin Israela da kuma Palasdinawa.

Taron wanda ake sa ran gudanarwa nan da wata daya mai zuwa, kasar Masar tuni ta furta cewa, a shirye take ta dauki nauyin gudanar dashi.

Sakatariyar harkokin wajen na Amurka dai ta kai ziyara ne wasu kasashe na yankin gabas ta tsakiyar, don dawo da daftarin zaman lafiyar nan na gabas ta tsakiya cikin hayyacin sa, a kokarin da ake na ganin an sami zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya.