Sabon salon siyasar Jam´iyyar ANC | Labarai | DW | 16.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon salon siyasar Jam´iyyar ANC

Jam´iyyar ANC a Afrika ta Kudu ta fara babban taron ƙolinta na wuni huɗu, da zai haifar da sabon shugaban Jam´iyyar na gaba. Ana dai wannan takara ne a tsakanin shugaba Thabo Mbeki da kuma tsohon mataimakinsa Jacob Zuma. Takarar shugabannin biyu, a yanzu hak ata haifar da darewar Jam´iyyar izuwa gida biyu. Duk wanda ya zamo sabon shugaban, bisa al´ada shi ya kann kasance shugaban ƙasar ta Africa ta Kudu. Duk da zarge-zargen cin hanci da rashawa daya dabaibaye tsohon shugaban, rahotanni sun ce Jacob Zuma ka iya samun nasarar lashe wannan zaɓe. Hakan dai nada nasaba ne da karɓuwarsa a tsakanin talakawa da kuma ma su fada aji a Jam´iyyar ta ANC.