Sabon salon siyasar dake tsakanin Iran da Amirka | Labarai | DW | 11.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon salon siyasar dake tsakanin Iran da Amirka

Shugaba Mahmud Ahmadinejad na Iran ya ce yana nan akan bakansa, dangane da buƙatar tattaunawar ƙeƙe da ƙeƙe da shugaba Bush, kan abubuwan dake faruwa a Duniya. Ahmadinajed ya faɗi hakan ne yayin da yake zantawa da ´yan jaridu a birnin Tehran. Irin wannan tattaunawa a cewar shugaban na Iran, abace da za ta taimaka, wajen warware wasu matsaloli da Duniya ke ci gaba da fuskanta. A watan satumba na shekarar data gabata Iran ta miƙa wannan tayi ga Amirka. A tun wancan lokaci mahukuntan na Washinton su ka yi watsi da wannan tayi.