1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon salon kasashen Latin Amirka na raya kasa

Ibrahim SaniDecember 10, 2007
https://p.dw.com/p/CZY0

Shugaba Hugo Chavez da wasu takwarorinsa shidda a Latin Amirka, sun ƙaddamar da wani sabon Banki na raya ƙasashen yankin. Bankin da akayiwa laƙabi da suna Banco del Sur, an ƙaddamar da shi ne da kuɗi wuri na gugar wuri har Dolar Amirka biliyan bakwai. Rahotanni sun shaidar da cewa Bankin zai dinga bawa ƙasashen rance mai matsakaicin ruwa a cikinsa, sabanin irin wanda Bankin Duniya ke bayarwa.Ƙasashen dake cikin wannan shiri sun haɗar da Argentina da Bolivia da kuma Brazil. Ragowar su ne Ecuador da Paraguay da kuma Venezuela.