1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon sakon Osama ga Amurka

Sabon sako da Osama bin Laden ya aika a yau jumaa,ya jinjinawa Abu Musab al Zarqawi da aka kashe,yana mai cewa kungiyarsa ce ta baiwa zarqawi umurnin kashe duk wani wanda ke goyon bayan Amurkawa a Iraqi.

Cikin sakon na tsawon mintuna 19 bin Laden ya bukaci shugaba Bush daya mika gawar Zarqawi ga iyalansa,yana mai karawa da cewa,zamu ci gaba da yaki da ku da abokanku a koina kuke,a iraqi ne ko Afghanistan,Somalia da Sudan,har sai kun kwashi kunya a hannun riga kun koma kasashenku.

Wannan shine sako karo na hudu da Osama ya aike cikin wannan shekara,sai dai jamian Amurka sunce basu tabbatar da ko muryar Osama bace a sakon na yau.