Sabon sakataren Majalisar Dinkin duniya ya fara aiki | Labarai | DW | 01.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon sakataren Majalisar Dinkin duniya ya fara aiki

Ban Ki Moon na kasar Koriya ta kudu ya karbi ragamar shugabancin MDD a matsayin sakatar janar na 8.

Dan shekaru 62 Ban ki Moon ya samu nasara ne bisa kann wasu yan takara 6 da suke neman kujerar sakatare janar na MDD.

Ban yace zai yi aiki tukuru wajen samarda karin zaman lafiya a duniya.

A daren jiya ne Kofi Annan ya kammala waadinsa na sakatare janar na MDD bayan shekaru 10.