Sabon saƙon bam | Labarai | DW | 04.11.2010
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon saƙon bam

An sake tura sabon saƙon bam zuwa ofishin jakadancin Faransa a Athens

default

Jami'an tsaro a Athens

'Yan sanda a ƙasar Girka sun ce sun gano wani saƙo mai bam wanda aka aike da shi a ofishin jakadancin ƙasar Faransa, wanda kuma ke zaman na 14 da aka aike a cikin mako.

Jami'an tsaron sun ce ma'aikatan ofishin sune suka sanar da su dangane da saƙon wanda akansa aka rubata cewa shugaban wani cocin orthodox ne ya aike da shi wanda aka dukukune da bam.

Wannan sanarwa dai da aka bayyana ta zone a daidai lokacin da aka yi ƙoƙarin kawar da wani yunƙurin a cikin saƙonnin bam 13 da aka aike a Faransa da Italiya da kuma Jamus.

Hukumomin tsaro dai a ƙasar Turkiya sun kama wasu matasa waɗanda ake zargin suna da hannu a cikin lamarin.

Mawallafi: Abdurrahaman Hassane

Edita: Umaru Aliyu

 • Kwanan wata 04.11.2010
 • Mawallafi Tijani Lawal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/PyPC
 • Kwanan wata 04.11.2010
 • Mawallafi Tijani Lawal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/PyPC