1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon saƙon Alƙa'ida

December 30, 2007
https://p.dw.com/p/Ci9L

Ƙungiyar Alƙa’ida ta Osama bin Laden ta sake aikewa da wani saƙo ta yanar gizo. Rahotanni sunce sakon na mintuna 56 yayi gargaɗi ne ga musulmin Iraki da kada su goyi bayan gwamnatin ƙasar mai goyon bayan Amurka. Muryar da tayi maganar ta kuma yi suka ga gwamnatin Saudiya game da abinda ta kira zagon ƙasa da ta yi wa Hamas. Tun farko a ranar Asabar ma’aikatar harkokin cikin gida ta Iraƙi tace tasirin Alƙa’ida tsakanin sojojin sa kai na ya ragu matuƙa,inda aka samu raguwar kashi 70 cikin ɗari na harkokin sojojin sa kai a ƙasar. Jami’an yaƙi da ta’adanci na Amurka sun ce suna duba tabbacin wannan saƙo.