A kalla mutane 36 ne aka hallaka yayin da 80 suka jikka ta
September 27, 2015Talla
Mai magana da yawun wata tawagar musulmai a yankin da rikicin ya faru Osmane Abakar yace, yamutsin ya kaure ne bayan gano wata gawa ta musulmi da ya mutu a wani masallaci dake a bangaren Kristocin, wanda hakan ya harzuka musulmin kai wani hari akan kristocin yankin a ranar a sabar.
Suma daga bisani Kristocin suka mayar da martani a ranar lahadin nan da yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Jami'an lafiyar birnin Bangui na kasar suka ce tuni aka fara kulawa mutane 80 din da suka sami raunuka a asibiti a yayin da 36 suka rigamu gidan gaskiya.
Tuni dai mahukuntan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar dake fuskantar tashe -tashen hankulan addini ta ayyana dokar tabaci a yankin da al'amarin ya faru.