Sabon rikici ya barke a Gaza | Labarai | DW | 26.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici ya barke a Gaza

An samu barkewan sabon fada tsakanin kungiyoyin dake adawa da juna a yankin palasdinawa watau Hamas da Fatah yau,A kalla mutasne 6 suka rasa rayukansu lokacinda dubban magoya bayan kungiyar Hamas sukayi wani gangami na jerin gwano akan titunan zirin Gaza,domin nuna farin cikinsu da zagayowar ranar cikan shekara guda na Hamas akan kujerar mulkin yankin,bayan nasaran da suka samu akan kungiyar Fatah ta shugaba Mahmoud Abbas.Wannan sabon rikicin yazo ne adaidai lokacin da shugaba Abbas da shugabannin na Hamas ke kokarin kafa gwamnatin hadaka a yankin.A birnin Davos dayajke halartan taro dai,shugaba Abbas yace nanda yan makonni zaa cimma daidaituwa,koda yake injishi rashin cimma tudun dafawa zai tilastashi shirya zabe da wuri a yankin.