1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici ya ɓarke a gabashin Kongo

Dubun dubatan fararen hula sun tserewa wani kazamin fada tsakanin sojojin sa kai da ´yan tawaye a wani lardi dake gabashin kasar JDK. Rahotanni daga ciki da wajen garin Bunagana mai nisan kilomita 50 arewa maso gabashin birnin Goma na arewacin lardin Kivu na cewa wani mummunan rikici ya barke a yankin. Sojojin gwamnati ba su shiga cikin wannan fadan ba wanda ya barke a wani yanki da ya kasance karkashin ikon ´yan tawaye tun kimanin watanni biyu da suka wuce. To sai dai sun dade suna shirye shiryen kaddamar da farmaki akan sansanonin ´yan tawaye. A kuma halin da ake ciki kasar Uganda makwabciyar Kongon, ta girke karin sojoji akan iyakar suna cikin shirin ko-takwana idan fadan ya bazu zuwa yankin ta.