Sabon rikici a zirin gaza | Labarai | DW | 25.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rikici a zirin gaza

Nahost

Dakarun sojin Izraela sun kaddamar da somame a yankin Zirin Gaza,sakamakon harin da sojojin sakai na palasdinu suka kai musu akan iyakar yankin.A wannan harin dai akalla palasdinawan 3 da yahudawa 2 ne,suka rasa rayukansu ,a kusa da kann iyakar kerem shalom.Hafsan sojin Izraela ya bayyana cewa ,daya daga cikin sojojin da da palasdinawan suka cafke na raye.Wannan shine rikici mafi tsanani a yankin ,tun bayan da dakarun Izraelan suka janye daga zirin gaza a watan satumban daya gabata.Prime minista Izraela Ehud Olmert ya zargi gwamnatin hamas da shugaba mahmud Abbas akan wannan harin .Tuni dai shugaban Palasdinawa Abbas yayi Allah wadan harin da sojin sakan suka kai.