Sabon rikici a Nepal
April 7, 2006Talla
Daruruwan dalibai ne suka kona wani ofishin aikeawa da wasiku atre da jifar yan sanda a dake kokarin korarsu a birnin Kathmandu na kasar Nepal,a kwana na biyu na zanga zangar adawa da gwamnati.
Daliban da sauran yan adawa na kasar dai sun suna bukatar a sauya gwamnatin kasar.
A yau din dai kamar yadda ya faru jiya yan sanda sunyi amfani da borkonon tsohuwa wajen kwantar da wannan tarzoma kwana na biyu a jere a kasar ta Nepal.
Shugabbanin adawa sunce an tsare magoya bayansu 150 a cikin rikicin na yau.