1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici a Jos

March 12, 2010

Kisan kiyashin da ya wakana a Jos ƙarshen makon da ya wuce na daga cikin batutuwan Afirka da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/MR96
Rikicin addini a Jos, NijeriyaHoto: AP

A cikin rahoton da ta gabatar ƙarƙashin take: "Yaɗuwar Ƙurar Tashe-Tashan Hankula" dangane da raikicin Jos, jaridar Der Tagesspiegel ta ambaci Matthias Basedau daga cibiyar nazarin al'amuran duniya da na yankuna dake birnin Hamburg Giga a taƙaice inda yake bayanin cewar:

Nigeria Unruhen Militär bei Jos
Sojoji a fafutukar lafar da ƙurar rikici a Jos, NijeriyaHoto: AP

"Ɓillar tashe-tashen hankulan, wanda shi ne mafi muni tun bayan kisan kiyashin da aka fuskanta a shekara ta 2001, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane dubu, a haƙiƙa ta kan biyo-bayan wasu aika-aika ne da suka gabata. Amma ainihin musabbabin rikice-rikicen shi ne gwagwarmayar dake akwai tsakanin ƙabilu daban-daban a fafutukar neman kyakkyawan matsayi na siyasa da tattalin arziƙi. Kuma kasancewar sojoji sun kasa ba wa jama'a kariya bayan kisan kiyashin da ya afku watan janairun da ya wuce, bisa ga ra'ayin Matthias Basedau, wata alama ce ta raunin Nijeriya, kamar yadda jaridar ta Der Tagesspiegel ta rawaito."

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta mayar da hankali ne akan kakkaɓe mashawarcin tsaro Sarki Mukhtar a Nijeriya, inda take cewa:

"Tare da kakkaɓe mashawarcinsa akan al'amuran tsaro Jonathan Goodluck ya mayar da martani akan zargin da ake wa jami'an tsaro, waɗanda harin da aka kai wa wasu ƙauyuka uku na kiristoci a Jos ya zo musu a ba zata. Ayar tambaya a nan dai shi ne ta yaya ne wasu ɗaruruwan mutane a cikin ɗamarar makamai suka samu kafar kusawa ƙauyukan na Zot da Dogo Nahawa da Ratsat duk da dokar hana fitar dare dake ci tun bayan tashin-tashinar watan janairun da ya wuce."

A zaɓen da aka gudanar a ƙasar Togo dai, an yi iƙirarin cewar shugaba mai ci Fature Gnassingbe shi ne yayi nasara inda ya lashe sama da kashi sittin cikin ɗari na jummular ƙuri'un da aka kaɗa, kuma masu sa ido na gamayyar tattalin arziƙin yammacin Afirka ECOWAS sun ce zaɓen an gudanar da shi tsakani da Allah ko da yake sun bayyana tababa game da takardun ƙuri'un da basu da lambar rajista, abin da zai iya saƙaƙe maguɗi, a cewar jaridar Fankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta ƙara da cewar:

Togo Demonstration Wahlen
Masu zanga-zangar adawa da sakamakon zaɓenHoto: AP

"Suma masu sa ido na Ƙungiyar Tarayyar Turai sun bayyana irin wannan tababa, musamman ma wajen danƙa wa hukumar zaɓe sakamakon ƙuri'un daga rumfunan zaɓe, wanda babu wata kafa ta bin diddiginsa a cewar Michael Gahler, shugaban tawagar sa ido ta Ƙungiyar Tarayyar Turai."

Akwai alamar karya guiwar ƙungiyar FDLR ta 'yan tawayen Hutu dake da ikon wasu yankuna na gabacin ƙasar Kongo take kuma da hannu a ta'asar kisan kiyashin da ya wakana a ƙasar Ruwanda a zamanin baya, kamar yadda askarawan kiyaye zaman lafiya na MONUC suka nunar. Jaridar Die Tageszeitung tayi nazari akan haka tana mai cewar:

"Idan har an ci gaba akan manufar gurguncewar ƙungiyar FDLR, to kuwa ba shakka Majalisar Ɗinkin Duniya zata iya buga ƙirji ta ce ta cimma nasarar manzancinta kuma tana iya fita daga ƙasar Kongo. Bisa ga dukkan alamu dai shugaba Joseph Kabila alla-alla yake yi ya ga askarawan majalisar sun bar ƙasar kafin zaɓen da aka shirya a watan yunin shekara ta 2011."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Halima Balaraba Abbas