1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Suleiman Babayo
May 30, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe daruruwan mutane a wannan wata na Mayu da muke ciki, kana wasu dubbai sun tsere daga gidajensu a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/2dq5v
Zentralafrikanische RepublikTrauer in Bangui
Hoto: Getty Images/AFP/E. Dropsy

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa sabon rikicin da ya barke a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, yayin da wasu kimanin 88,000 suka tsere daga gidajensu, tun daga farkon wannan wata na Mayu da muke ciki. Kasar wadda take sahun gaba a cikin kasashen 'yan rabbana ka wadata mu, ta sake samun kanta cikin wannan hali yayin da take kokarin murmurewa daga shekaru uku na yakin basasa tsakanin Musulmi da kungiyar tsageru ta mabiya addinin Kirista.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da  cewa yanzu haka akwai fiye da 'yan gudun hijira a cikin kasar fiye da 500,000, yayin da fiye da 120,000 suka tsere zuwa Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Sabon rikicin na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na ritsawa da fararen hula.