Sabon rikici a Darfur | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 09.03.2010
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sabon rikici a Darfur

Wani sabon rikici ya sake kunno kai a lardin Darfur mako ɗaya kacal bayan rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta

default

Bikin rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta kan rikicin Darfur a Doha

Daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afirka a wannan makon har da mawuyacin hali na tashe-tashen hankula da aka sake shiga a lardin Darfur na kasar Sudan duk da yajejeniyar tsagaita wutar da aka cimma baya-bayan nan. A cikin nata rahoton dai jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Mako ɗaya kacal bayan rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan tawayen JEM a ƙasar Sudan murna ta sake komawa ciki. Domin kuwa kwana ɗaya bayan wannan biki, a daidai lokacin da shugaba Al-Bashir ke batu a game da kawo ƙarshen yaƙin Darfur a wani yaƙin neman zaɓe a yankin El-Fashir dake arewacin Darfur jiragen saman yaƙinsa suka fara kai sabbin hare-hare a Jebel Mara dake Darfur. Ɗaya matsalar kuma ita ce fitowa fili da ƙungiyar JEM tayi tana mai cewar ba zata rattaɓa hannu kan wata yarjejeniya ta zaman lafiya ba, wai saboda shiga tattaunawa da gwamnati tayi tare da sauran ƙungiyoyin tawaye da ba su ga maciji da juna."

A ƙasar Cote d'Ivoire akwai kyakkyawan fata na kawo ƙarshen zub da jini a ƙasar, inda 'yan hamayya suka bayyana shirinsu na bai wa sabuwar gwamnati da za a naɗa haɗin kai bisa manufa, kamar yadda jaridar Süddeutsche Zeitung ta nunar ta kuma ƙara da cewar:

Elfenbeinküste Friedensverhandlungen in Südafrika

Tattaunawar sasanta rikicin Cote d'Ivoire a Afirka ta Kudu

"Wannan shawara da 'yan hamayya suka ɗauka zata taimaka wajen lafar da ƙurar wasu sabbin tashe-tashen hankula da ka taso, waɗanda kuma zasu iya zama barazana ga shawarwarin tabbatar da zaman lafiyar ƙasar ta yammacin Afirka. Ƙasar ta Cote d'Ivoire dai, wadda a zamanin baya ta zama abar misali dangane da bunƙasar tattalin arziƙi a yammacin Afirka, ta zunduma cikin yaƙin basasa a shekara ta 2002, kuma sabon zaɓen da ake shirin gudanarwa, ana fata zai taimaka ta fita daga cikin mawuyacin halin da tayi shekara da shekaru tana fama da shi."

A ƙasar Nijer an yi marhabin lale da shawarar da gwamnatin soja ta tsayar game da naɗa gwamnatin wucin gadi da farar hula da kuma alƙawarin cewar gwamnatin ba zata shiga takarar zaɓen da za a gudanar nan gaba ba. Jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi tana mai cewar:

"A dai halin da ake ciki yanzu wajibi ne a jira a ga yadda al'amura zasu kasance nan gaba. Domin kuwa kyakkyawan yanayin ƙasar ba ya danganta ne da al'amuran siyasa ba. Babban abin dake taka rawa shi ne ci-maka. Domin kuwa akwai fargabar cewa ƙasar ta Nijer zata iya fuskantar mummunar matsalar yunwa irin shigen ta shekara ta 2005, muddin ba tashi tsaye aka yi akan tinkari wannan matsala ba to kuwa murna zata iya komawa ciki a game da sabuwar alƙiblar da aka nufa."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal

 • Kwanan wata 09.03.2010
 • Mawallafi Tijani Lawal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/MNpl
 • Kwanan wata 09.03.2010
 • Mawallafi Tijani Lawal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/MNpl