Sabon rahoton kungiyar Transparency International | Labarai | DW | 18.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon rahoton kungiyar Transparency International

Kungiyar nan da ke yaki da matsalolin cin hanci wato Transparency International ta ce Jamus ba ta samu wani ci-gaba na a zo a gani ba a yaki da cin hanci da rashawa a cikin kasar. Sabon jerin sunayen kasashe 159 da wannan matsala ta yiwa katutu da kungiyar ta bayar ya nuna cewa Jamus na matsayi na 16, yayin da kasashen Iceland, Finnland da New Zealand ke a matsayi na farko tsakanin kasashen duniya da ba sa fama da ayyukan cin hanci da karbar rashawa. Kungiyar mai zaman kanta ta ce a wannan marra da muke ciki cin hanci da karbar rashawa ya fi yin muni a kasashen Turkmenistan da Bangladesh da kuma Chadi.