Sabon rahotan Amnesty kan Fyaɗe wa Mata ′yan gudun hijira | NRS-Import | DW | 30.09.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Sabon rahotan Amnesty kan Fyaɗe wa Mata 'yan gudun hijira

Sama da 'yan gudun hijirar Darfur dubu 260 ne ke sansanoni 12 a yankin gabashin Chadi

default

Mata da 'yan mata masu gudun hijira na lardin Dafur na cigaba da fuskanatar cin zarafi ta hanyar Fyaɗe, a sansanonin gudun hijira da wajensu dake yankin gabashin ƙasar Tchadi, duk kuwa da kasancewar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗunkin Duniya dake yankin.

Wannan zargin na kunshe ne a sabon rahotan ƙungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta Amnesty International.Mai taken "ba mu da wurin zama anan, cin zarafin mata a sansanin 'yan gudun hijira a gabashin Tchadi", ƙungiyar tace a kowane wayewan gari mata da yara mata na fuskantar cin zarafi ta hanyoyi daban-daban daga ɓangaren mazauna kauyuka dake makwabtaka, a wasu lokuta kuma daga sojojin gwamnatin Tchadi.

Jami'ar gudanar da bincike kan Sudan Rania Raji tace mata dake sansanin na yankin gabashin Tchadi na cikin tashin hankali sanadiyyar rashin tsaro.

Flüchtlingslager im Darfur

Sansanin 'yan gudun hijira

" ta ce abunda muka gano shine, akwai karuwar barazanar rashin tsaro,wanda ya bar mutanen su kula da kansu. Saboda babu wata kariya a kewayen da suke.Hakan ne yasa suke fuskantar kai musu hare-hare daga ɓangaren 'yan adawa, 'yan fashi da kuma sojojin gwamnati"

Rahotan dai ya yi bayanin cewar 'yammta na fuskantar cin zarafi hatta daga ɓangaren malaman makarantan dake koyar dasu, bayan yi musu barazanr faɗar dasu a jarrabawa.

Mataimakin Direktan Amnesty dake kula da shiyyan Afirka Tawanda Hondora, yace kowa yasan cewar Matan da kan shiga jejin dake wajen sansanonin domin neman itacen girki, da kuma ruwan sha na fuskantar barazanar yi musu fyaɗe. Sai dai abunda mutane basu sani ba shine , koda a cikin sansanonin 'yan gudun hijiran ma, matan basu da wata kariya. Kasancewar Matan na fuskantar barazanar fyade daga ɓangaren Iyalansu, wasu 'yan gudun hijiran, da ma ma'aikatan ƙungiyoyin bada agaji, waɗanda hakkin daya rataya a wuyansu shine kare waɗannan Matan.

" Haki ya rataya a wuyan sojin kiyaye zaman lafiya su samarda kariya, akarkashin tallafin ayarin dakaru da 'yansandan gwamnatin tchadi, wadanda su ayyukansu shine kare sansanonin 'yan gudun hijiran.Sai suna fama da matsaloli na rashin jami'ai da kuma kayayyakin aiki".

Dayawa daga cikin matan dake fuskantar matsalar cin zarafin dai, suna ganin cewar jami'an tsaron basa taɓuka musu komai, musamman wajen samar musu kariya.

Kuma baya ga hakan, yawancin waɗanda ke aikata wannan miyagun ayyukan, ba a cika gurfanar dasu a gaban hukuma ba, ballantana ayi maganan hukunta su.

Adangane da hakane ƙungiyar Amnesty international take kira dangane ɗaukar matakan da suka wajaba na dakatar da cin zarafin matan.Kamar yadda Rania Raji tayi bayani..

"ta ce muna kira ga waɗanda abun ya rataya a wuyansu, kama daga sojojin tabbatar da zaman lafiya, da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, musamman kuam sojin gwamnatin Tchadi , duk kuwa dacewar ƙungiyoyin adaw sune keda alhakin mafi yawan wannan zargi na fyaɗe da fashi, ya kamata su san cewar su ya kamata su samarwa da fararen hula kariya"

Darfur UNAMID

Dakarun kiyaye zaman lafiya

Rahotan Amnesty yayi nuni dacewar, amfani da hanyoyin gargajiya wajen sasanta batutuwan da suka shafi cin zarafin mata kamar Fyaɗe, basa haifar da kyakkyawan sakamako, wanda a wasu lokuta ma ke daɗa ruruta wutan cigaban matsalar.

Ƙungiyar Amnesty tace yawancin matan aure da aka yiwa fyaɗe suna fuskantar fyaɗe daga wajen mazajensu, ayayinda su kuwa 'yan matan sukan rasa darajarsu, wanda ya kan jagoranci su rasa mazajen da zasu auresu.

Mawallafiya: Zainab Mohammad

Edita: Ahmad Tijani Lawal