Sabon lale na nemo bakin zaren warware rikicin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 20.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon lale na nemo bakin zaren warware rikicin nukiliyar Iran

Wakilin kasar Iran a fannin makami na nukiliya, wato Ali Larjani ya isa birnin Mosko na Russia don tattaunawa da wakilan kasashen turai game da aniyar kasar na mallakar makamin nukiliya.

Wannan dai tattaunawa tazo ne kwanakin kadan bayan taron kasashe shidda masu fada a duniya ya tashi ba tare da cimma wata matsaya guda ba a game da rikicin nukiliyar ta Iran.

Duk kuwa da irin furuce furuce na damuwa dake fitowa daga kasar Amurka a game da wannan batu, sakataren harkokin wajen Biritaniya Jack Straw cewa yayi baya zaton Amurka zata dauki mataki na soji akan kasar ta Iran.

Jack Straw , wanda ya fadi hakan a jiya, ya kuma bayyana shakkun sa cewa kasar Iran da wuya ta daina ci gaba da matakin data dauka na sarrafa sanadarin na Uranium, izuwa wa´adin karshen watannan da Mdd ta deba mata.

A dai karshen watan nan ne kwamitin sulhu na Mdd, yace hukumar IAEA ta kawo mata rahoton aiwatar da wannan umarni ko akasi n haka data bawa kasar ta Iran , don sanin matakin da zata dauka na gaba.