1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon Kudurin Ciniki Tsakanin Kasashen Turai Da Kasashe Masu Tasowa

October 20, 2004

Kungiyar Tarayyar Turai zata sauya salon cinikayyarta da kasashe masu tasowa tun daga shekara ta 2006

https://p.dw.com/p/BvfP

Kantoman hukumar zartaswa na kungiyar tarayyar Turai akan manufofin ciniki Pascal Lamy ya gabatar da tsarin ba da fifikon cinikin ga kasashe masu tasowa a can birnin Brussels, shelkwatar kungiyar tarayyar Turai. Ya ce kungiyar zata yi biyayya ga zartaswar baya-bayan nan ta Kungiyar Ciniki ta Duniya WTO. Nan gaba za a gabatar da wani tsari ne mai saukin aiwatarwa sakamakon kurakuran da aka rika cabawa a zamanin baya wajen ba wa kasashe masu tasowan fifiko saboda sarkakiyar tsarin da aka rika tu’ammali da shi. Nan gaba za a yi tu’ammali ne da wani tsari mai matakai guda uku. Matakin farko ya tanadi kayyade kudaden kwasta da misalin kashi 3.5% dangane da dangin kayayyakin da suka hada da motoci da tufafi da darduma da wasu kayan amfanin noma da na lantarki. A baya ga haka ragowar kayayyakin ana iya shigowa da su zuwa kasashen Turai ba tare da kwasta ba. Shi kuwa mataki na biyu ya jibanci samfurin kayayyaki kimanin 7200, wadanda za a cimma daidaituwar ciniki akansu tare da kasashen dake biyayya ga yarjeniyoyi na kasa da kasa akan girmama hakkin dan-Adam da hakkin ma’aikata da kuma bin nagartattun manufofin kare kewayen dan-Adam. Sannan mataki na uku zai shafi kasashe 50 ne da suka fi talauci a duniya wajen ba su damar shigo da kayayyakinsu ba tare da kwasta ko kayyade musu kaso ba, amma banda cinikin makamai. Daya daga cikin ka’idojin cin gajiyar wannan manufa shi ne kasancewar yawan abin da kasar da lamarin ya shafa take shigowa da shi zuwa kasashen Turai bai zarce kashi 15% ko kuma kashi 12.5% dangane da kayan saka ba. Lamy ya ce kasar China ita ce tafi cin gajiyar lamarin saboda ta fi kowace kasa fitar da kayan saka zuwa ketare. Kazalika bisa ta bakin kantoman hukumar zartaswar ta KTT akan al’amuran ciniki kasashe masu tasowan da zasu fi amfana da manufar debe kudaden kwasta din gaba daya sune masu hannu a yarjeniyoyi 25 na kasa da kasa akan hakkin dan-Adam da kewayen muhalli da nagartattun manufofi na demokradiyya da haramta ayyukan yara kanana. Lamy na tattare da imanin cewar kasar Pakistan zata fara cin gajiyar wannan manufa tun daga shekara ta 2006, a yayinda kasashe kamarsu Koriya ta Arewa da Bailorusshiya zasu sha fama da wahala. A yanzu ana sauraron majalisar ministoci da kuma majalisar Turai domin su albarkaci wannan sabuwar shawara ta yadda zata fara aiki tun daga daya ga watan janairun shekara ta 2006. Duk wata kasar dake bukatar shiga a dama da ita wajibi ne ta gabatar da takardunta, sannan su kuma kasashen ACP da suka hada da na Afurka da Karibiya da kuma Pacific suke da damar gabatar da nasu takardun da sunan kungiya.