Sabon Kasset ɗin bil Laden | Labarai | DW | 23.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon Kasset ɗin bil Laden

Wani Kasset mai ɗauke da sautin murya da aka danganta cewa ya fito daga shugaban ƙungiyar al-Qaída Osama bin laden da kuma aka sanya a gidan Talabijin ɗin Aljazira yayi kira ga ƙungiyoyin yan tawaye a Iraqi su kawar da banbance banbancen dake tsakanin su, su haɗa ƙarfi wuri guda domin cigaban ƙasar ta Islama. Muryar ta kuma yi gargaɗi ga yunƙurin abokan gaba na raba kawunan ƙungiyoyin ta hanyar dasa yan leƙen asirin su. Manazarta sun ce sautin muryar ta yi kama da ta Osama bin Laden sai dai baá haƙiƙance ba.