1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon harin 'yan tawayen Chechniya

June 22, 2004

A jiya da dare 'yan tawayen Chechniya suka kai farmaki tare da halaka mutane 46 abin da ya hada har da ministan cikin gida na Ingusheshiya

https://p.dw.com/p/Bvin
Ma'aikatar cikin gida ta Ingusheshiya bayan farmakin da 'yan tawaye suka kai
Ma'aikatar cikin gida ta Ingusheshiya bayan farmakin da 'yan tawaye suka kaiHoto: AP

Bisa ga dukkan alamu dai jami’an siyasa, abin da ya hada har da na kasashen yammaci, ba su da zurfin tunani da hangen nesa. Domin kuwa da yawa daga cikin jami’an siyasar ko dai sun manta ko kuma sun yi watsi da gaskiyar cewar a wasu ‚yan tsirarun shekarun da suka wuce an fuskanci kazamin fada tsakanin ‚yan tawayen Chechniya da sojan kasar Rasha. Amma fa ba a tashi tunawa da wannan rikici sai idan an fuskanci ta’asa irin shigen wadda ta wakana a jiya da dare. Ummal’aba’isin yakin na Chechniya kuwa shi ne fafutukar neman ikon cin gashin kai da mazauna yankin ke yi daga tarayyar Rasha. Amma a yanzu wasu dalilan sun karu akan wancan. Misali neman ramuwa da ‚yan Chechniya suke yi akan radadin rashin adalcin da suka sha fama da shi a hannun sojojin Rasha da kuma neman kakkabe janhuriyar Chechniya dake da rinjayen Musulmi daga Rashawa ‚yan Kirista. A baya ga haka akwai gwagwarmayar kama madafun iko da neman yada angizon masu safarar miyagun kwayoyi da cinikin makamai. Shi kuwa shugaban Rasha Vladmir Putin kokari yake yi ya nuna wa duniya cewar yana da cikakken ikon tabbatar da zaman lafiyar Chechniya. Amma fa tilas murnarsa ta koma ciki ta la’akari da harin da dakarun ‚yan tawayen Chechniya suka kai kan Ingusheshiya mai makobtaka da Chechniyar. A cikin takaici sojojin Rasha suka sa ido suna masu kallon yadda ‚yan tawayen su kimanin 200 suka kai farmaki kan ma’aikatar cikin gida da wasu kafofi na gwamnati a garin Nasran ba tare da sun tabuka kome ba. Domin kuwa kafin sojojin na Rasha su ankara tuni bakin alkalami ya bushe. A yanzun abin da zai biyo baya, kamar yadda aka saba gani shi ne matakin farautar ‚yan tawayen, inda sojojin Rasha da kawayensu na Chechniya zasu rika bi kauye-kauye domin bin diddigin ‚yan tawayen. To sai dai kuma ko da yake mai yiwuwa a cafke wasu ‚yan kalilan daga cikinsu, amma tuni akasarin ‚yan tawayen suka buya. Kuma a karshe farar fula ne zasu sha fama da radadin wannan mataki. Kiyayyar sojojin mamayen na Rasha sai dada karuwa take yi a zukatan jama’ar Chechniya ta yadda da wuya a kawo karshen tashe-tashen hankulan da ake fama dasu. Da yawa daga shuagabannin Chechniya na korafi a game da yadda kasashen yammaci suka yi fatali da rikicin yankin da ya ki ci ya ki cinyewa. Daya daga cikin dalilan haka kuwa shi ne kasancewar kafofin yada labarai na kasashen na fargabar tura wakilansu zuwa yankin na Kaukasiya saboda su kan fuskanci muzantawa daga bangaren ‚yan tawayen da kuma bangaren sojojin Rasha. A halin yanzu haka ba wanda ya san adadin ‚yan jaridar kasashen yammaci da aka sace ko kuma aka kashe lokacin da suke bakin aikinsu na ba da rahoto akan yakin Chechniya. Wannan rikici na Chechniya ka iya gurbata yanayin hadin kan yaki da ta’addanci tsakanin Amurka da Rasha. A yayinda Rasha ke yi kamar dai ita din wata kasa ce dake bin tafarkin demokradiyya da girmama hakkin tsiraru, su kuma kasashen yammaci a nasu bangaren yi suke kamar dai sun yarda da gaskiyar hakan.