1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Shabab ta kai sabon hari a Kenya

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 13, 2015

A karo na biyu cikin watanni biyar 'yan ta'adda sun kai hari a kan ayarin motocin wani gwamna a arewacin kasar Kenya tare da hallaka mutane uku.

https://p.dw.com/p/1Eqi2
Hoto: picture-alliance/dpa/Said Yusuf Warsame

Jami'an 'yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin inda suka ce mutane biyar sun jikkata yayin harin kuma suna cikin matsanancin hali. Jami'in dan sandan da ya nemi a sakaya sunansa saboda ba a ba shi izinin yin magana da kafafaen yada labarai ba, ya ce maharan su akallah 20 sun budewa ayarin motocin gwamnan wuta da bindigogin atilare da rokoki. Tuni dai kungiyar al-Shabab ta Somaliya da ta saba kai hare-haren ta'addanci a kasashen Kenyan da Somaliya ta dauki alhakin kai harin, ta hanyar ba da sanarwa a gidan rediyon kungiyar. Harin dai na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan rantsar da sabon speto janar na 'yan sandan kasar biyo bayan ajiye aiki da tsohon speton ya yi sakamakon harin da 'yan ta'addan suka kai a garin Mandera a shekarar da ta gabata inda mutane 36 suka hallaka.