Sabon harin kunar bakin wake a Najeriya | Labarai | DW | 31.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin kunar bakin wake a Najeriya

Wata yarinya 'yar kunar bakin wake ta hallaka kanta a garin Banki da ke kan iyakar jihar Borno a Najeriya da Jamhuriyar Kamaru.

Hare-haren kunar bakin wake a jihar Bornon Najeriya

Hare-haren kunar bakin wake a jihar Bornon Najeriya

Yarinyar da aka kiyasta shekarunta da akalla 10, ta kashe kanta ne a wannan Talata 31 ga wannan wata na Janairu da muke ciki da misalin karfe 11.30 agogon Najeriya, yayin da ta yi kokarin shiga wani sansanin 'yan gudun hijira da ke garin na Banki. Shaidun gani da ido sun ce jami'an sojoji da ke wajen ne suka yi kokarin dakatar da ita tare da barazanar harbe ta kafin ta mika kai. 

An kuma ga jigidar boma-bomai shake jikinta kafin daga bisani ta tayar da su nan take, sai dai babu wani da ya mutu ko kuma ya jikkata sanadiyyar harin nata. An dai danganta hare-haren sari-ka-noke na yanzu da mataki na martani da mayakan Boko Haram ke dauka, sakomakon tsananin da suke fuskanta daga dakarun gwamnatin Najeriya. Garin Banki dai na da nisan kilomita 133 da Maiduguri babban birnin jihar Borno ta Najeriya.