Sabon harin kunar bakin wake a Iraki ya halaka akalla mutane 35 | Labarai | DW | 19.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon harin kunar bakin wake a Iraki ya halaka akalla mutane 35

Akalla mutane 35 sun rasu sannan kimanin 40 sun jikata a wani sabon harin kunar bakin wake da aka kai a kusa da birnin Bagadaza. Kamar yadda ´yan sanda suka nunar wani dan kunar bakin wake ya ta da bam da ya dana a cikin mota kuma ya tuka ta zuwa cikin gungun masu jana´izar wani babban malamin ´yan shi´at a kauyen Abu Saba dake kusa da birnin Baquba mai nisan kilomita 60 arewa maso gabashin Bagadaza. Da farko a yau asabar wani bam da aka dana cikin wata karamar mota ya halaka mutane 13 sannan ya jikata 21 a wajen babban birnin na Iraqi. Yanzu haka dai yawan wadanda suka mutu sakamakon hare haren kunar bakin wake a Iraqi a cikin kwanaki 3 da suka wuce ya kai mutum 130. A lokacin da yake magana a Koriya Ta Kudu Shugaban Amirka GWB yayi watsi da kiraye kiryaen da ´yan siyasar kasarsa ke yi na a janye dakarun Amirka daga Iraqi.