Sabon gwamnati a fiji | Labarai | DW | 08.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon gwamnati a fiji

Sabon shugaban soji na kasar Fiji ya nada gwamnatin wucin gadi. Komodore Frank Bai-ni-marama wanda aka rantsar satin daya gabata a matsayin prime minista, wanda yau sati hudu kenan bayan daya shugabanci juyin mulki a kasar, ya zabi jami’ai wadanda zasu taya shi gudanar da al’amuran kasar. Bai-ni-ramama wanda yace gwamnatin sa zai share fage domin kafa mulkin demokradiya, bai yi wani bayani akan lokacin da za’a gudanar da zaben kasar ba.