1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon Firimiya a Birtaniya

Bayan shekaru 13 suna wajen gwamnati yanzu jam'iyyar Conservative ta samu ɗarewa kan jagorancin gwamnatin ƙasar Birtaniya

default

David Cameron

An samu sabon Firayim minista a ƙasar Birtaniya, kuma a karo na biyu ke nan da aka kafa gwamnatin haɗin gwiwa tun bayan yaƙin duniya na biyu. David Cameron ya samu kai jam'iyarsa ta Conservative ga wannan muƙamin, bayan shekaru 13 suna matsayin 'yan adawa a harkokin ƙasar wanda take da tasiri a siyasar duniya.

Bayan kwanaki biyar ana kai kawo don samun kafa gwamnati a ƙasar ta Birtaniya, daga ƙarshe dai a yammacin jiya tattaunawa tsakanin jam'iyar Labour ta Gordon Brown da ta masu sassaucin ra'ayi na Liberal wanda ta zo ta ukku a zaɓen ƙasar, tattaunawar ta su ta watse, daga nan sai Gordon Brown ya jefar da ƙashe, ya buɗe ƙofa ga magajinsa. Sa'a guda bayan haka sarauniyar Ingila ta sanar da sunan sabon Firimiya.

Yanzu dai abinda Cameron zai fiskanta shine zaman sabuwar majalisar dokoki, abinda yace suna da ƙalubale a gabansu, wanda ya haɗa da batun tattalin arziki dake ɗingishi da sauran matsalolin rayuwa a ƙasar.

Don haka nake son kafa gwamnatin haɗaka tsakanin jam'iyyar Consevative da ta Liberal. Nick Clegg da ni mune shugabannin jam'iyun, kuma za mu warware banbance banbacen mu, don mu yi aiki mai kyawu wa ƙasarmu"

Ita ma dai jam'iyar ta Liberal ta gwammaci kafa gwamnati tare da ta Consevative, duk da cewa manufofin jam'iyyun sun banbanta. Yanzu dai jagoran Liberal zai tuntuɓi abokan tafiyarsa, domin dokar Birtaniya ba kamar ta ƙasar Jamus ba, inda ake baiwa abokan tafiya masu ƙaramin rinjaye manyan muƙamai, amma a Birtaniya duk jam'iyya mai yawan kujeru, itace take handame abunta. Misali yanzu dai za'a baiwa Clegg mataimakin Firimiya, muƙamin da bashi da wata tsoka, kusan ma ace na jeka nayika ne. Da a ƙasar Jamus ne kuwa, shi zai kasance ministan harkokin waje.

Amma dai ga abinda sabon Firimiyan yake cewa

"Babban ƙalubalen dake gabanmu shine tinkarar matsalolin, mu samu warwaresu da kuma samun al'umma ta amince da hakan, domin baki ɗaya mu samu biyan buƙata mai alfalu"

Waɗannan matsalolin dai sun haɗa da batun giɓin dake cikin kasafin kuɗin ƙasar, abinda kuma ke tsaye a zukatan masu kaɗa ƙuri'a.

Su dai 'yan jam'iyyar Labour, tun bayan da Brown ya sanar da ajiye aiki, basa yarda idonsu ya haɗu da kamar 'yan jarida, domin kuwa mulkin jam'iyyarsu na shekaru 13 ya zo ƙarshe.

NO FLASH Gordon Brown Wahl 2010

Gordon Brown

Brown yace "Ina sha'awar wannan muƙamin, bawai domin alfurma da kimar da yake da shi ba, waɗanda ni banaso, sai dai domin damar da zai bayar mutum ya tafiyar da ƙasar cikin adalci, da demokraɗiyya a yanayi mai ƙayatarwa"

Yanzu dai makomarsa a jam'iyar sa ta Labour, lokacine kawai zai iya nunawa, abinda 'yan majalisarsa ke cewa, bari dai muga abinda sabuwar gwamnati za ta haifar.

Mawallafa: Barbara Wesel da Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal