1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon Firimiya a Birtaniya

May 12, 2010

An naɗa David Cameron a matsayin sabon Firimiyan ƙasar Birtaniya, inda yanzu jam'iyar Labour ta kau daga gwamnati

https://p.dw.com/p/NLo1
Cameron da sarauniya Elizabeth IIHoto: AP

Sarauniyar Ingila  Elizabeth ta 2, ta tabbatar da naɗin David Cameron a matsayin sabon Firimiyan ƙasar, abinda ya kawo ƙarshen gwamnatin Labour na shekaru 13 kan mulkin ƙasar Birtaniya. An naɗa Cameron ne bayan da Gordon Brown ya sauka daga muƙamin. Ɗan shekaru 43 da haifuwa Cameron yace abinda ke gabansa shine kafa gwamnatin haɗin giwa tare da jam'iyar Liberal Demokrat dake ƙarƙashin shugabancin  Nick Clegg. Jam'iyar Consevative ta lashe zaɓen ƙasar da aka yi, to amma bai bata rinjayen kafa gwamnati ba ita kaɗai ba. Tuni dai shugabannin ƙasashen yamma waɗanda suka haɗa Barack Obama na Amirka da Angela Merkel ta Tarrayar Jamus da shugaba Sarkozy na Faransa suka suka taya Cameron murnar sabon muƙamin da ya samu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissu Madobi