Sabon Firaministan Rasha ka iya zama ɗan takarar shugaban ƙasa | Labarai | DW | 15.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon Firaministan Rasha ka iya zama ɗan takarar shugaban ƙasa

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce watakila sabon FM da aka nada, Viktor Subkov ka iya zama dan takarar shugaban kasar na gaba. Putin ya ce Subkov na daya daga cikin mutane biyar da ka iya tsayawa takarar a zaben shugaban kasa da zai gudana cikin watan maris mai zuwa. A jiya juma´a majalisar dokokin Rasha wato Duma tare da gagarumin rinjaye ta tabbatar da Subkov a matsayin magajin FM mai barin gado Mikahil Fradkov. Subkov ya fadawa majalisar cewa abin da zai ba wa fifiko shi ne ta da komadar tattalin arziki da karfafa ma´aikatar tsaro.