1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon fada ya barke a Somalia

Hauwa Abubakar AjejeDecember 20, 2006

Wani kazamin fada ya barke yau tsakanin dakarun gwamnati da magoya bayan kotunan islama a wasu kauyuka na kasar Somalia,yayinda bangarorin biyu ke ci gaba da neman kame muhimman wurare a kasar

https://p.dw.com/p/Btwy
Hoto: AP

Wannan fada ya barke ne yayinda jakadan Kungiyar Taraiyar Turai ya isa birnin Baidoa inda ya gana da manyan jamian kasar,a kokarinsa na ganin an tattauna tsakanin bangarorin biyu.

Komishinan taimako da ci gaba na kungiyar taraiyar turai Louis Michel,tuni ya gana da firaminista Ali Muhammad gedi da shugaban rikon kwarya Abdullahi Yusuf.

Hankula dai sun kara tashi cikin yan kwanakin nan a Somalia,musamman bayan waadin da kotunan islama suka baiwa kasar Habasha wadda dakarunta suke Somalia suna masu bada goyon baya ga gwamnatin wucin gadin,cewa su fice daga kasar cikin mako guda ko kuma su fuskanci hare hare.

To,wannan waadi dai tuni ya wuce a jiya talata ba tare da wani fada mai tsanani ba,sai dai fadan na yau ya nuna alamun yiwuwar ci gada da tashe tashen hankula a kasar.

Michel dai ya gana da jamian gwamnatin Somalia a birnin Baidoa a yau laraba, daga bisani ya wuce zuwa birnin Mogadishu,domin tattaunawa kuma da shugabannin kotunan islama.Kakakin Michel,Amadou Altafaj yace Michel yana kokari ne ya samarda tsagaita wuta cikin gaggawa.

Kungiyoyin islama da suka kame birnin Mogadishu a watan yuni yanzu suna rike da yawancin kudu maso tsakiyar kasar,kuma sun lashi takobin kaddamar da jihadi kan sojojin Habasha dake cikin kasar.

Kwararru akan harkokin Somalia sunce akwai yiwuwa sake barkewar yaki game da rikicin raba madafun iko tsakanin bangarorin biyu,duk da cewa MDD ta bukaci a aike da dakaru daga kasashen yankin domin samarda zaman lafiya.

Sai dai Ulf Tarlinden wani masani kan harkokin kasar ta Somalia anan Jamus,yace kuduri da MDD ta yanke game da kasar yana goyon bayan bangare daya ne.

masu lura da alamura dai sunce akwai hadarin bazuwar yaki a yankin na kahon Afrka,biyowa bayan zargin da Eritrea da Habasha sukeyiwa junansu.

Sai dai shugaban Eritrea Issaias Afeworki yayi watsi da batun cewa fada na iya bazuwa cikin kasashen yankin,a maimakon haka yayi gargadi ne ga Habasha wadda aka baiwa dakarunta waadin ficewa daga Somalia,cewa tana cikin hadarin sa kanta dumu dumu cikin rikicin kasar Somalia.