Sabon bidiyon Osama Bin Laden na farko cikin shekaru 3 | Labarai | DW | 08.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon bidiyon Osama Bin Laden na farko cikin shekaru 3

A cikin wani sabon bidiyo da aka nuna a jiya juma´a shugaban kungiyar ´yan ta´adda ta Al-Qaida Osama Bin Laden ya lashi takobin ci-gaba da fafatawa a Iraqi. Wannan dai shi ne karon farko cikin shekaru 3 da Bin Laden ya bayyana a cikin wani hoton bidiyo. Hukumomin leken asirin Amirka sun tabbatar da muryar kan faifayen da cewa ta Osama Bin Laden ce. Shugaban Amirka GWB ya ce bidiyon na Bin Laden na yin tuni da abin da ya kira wai wani hadari da duniya ke ciki. An fid da bidiyo din ne don yayi daidai da zagayowar shekaru 6 da hare-haren ta´addancin da aka kaiwa biranen New York da Washington a ranar 11 ga watan satumban shekara ta 2001. A kuma halin da ake ciki diraktan hukumar leken asirin Amirka CIA, Michael Hayden ya yi gargadin cewa hukumar sa ta yi imani cewa al-Qaida na shirin kai sabbin hare hare akan Amirkawa.