Sabon babin zumunci tsakanin Najeriya da Kamaru | Siyasa | DW | 03.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon babin zumunci tsakanin Najeriya da Kamaru

Ziyarar da ke zaman irinsa na farko cikin shekaru 25 dai, na zaman sabon fata ga makwabtan na sake gamewa wuri guda da nufin tunkarar matsaloli na rayuwa da cigaba

Wani rikici na kan iyaka da ma tsibiri na Bakassi ne dai ya kai ga farakka dangantaka a tsakanin tsofaffin kawayen kafin daga baya matsalar Boko Haram ta tilasta su sake fuskantar juna.

Ziyarar din da ta kalli shugabannin biyu share awoyi sama da biyu suna ganawar sirri dai, na da burin duban hanyoyin karasa tunkarar kungiyar ta taádda da kuma nazarin hada kai da nufin sake ginin kauyuka da biranen da suka sha ba dadi sakamakon matsalar.

A kalla yarjejeniyoyi kusan bakwai ne dai ake jin kasashen biyu zasu kai ga rattaba hannu a kai a fadar Garba Shehu da ke zaman kakakin gwamnatin ta Abuja.

A wannan Laraba ce dai ake saran shugabannin biyu zasu yi wani taro na hadin gwiwa da nufin sanar da irin jerin shawarin da suka yi nasarar kullawa a ziyarar da ke nuna alamun danyan ganye a tsakanin kasashen na Najeriya da ma Kamaru.

To sai dai kuma makomar rundunjar sojoji na hadin gwiwa a cikin tafkin Chadin da kuma kokari na kara tsaurara matakai na tsaron iyaka ne dai, ake saran zasu dauki hankali a tsakanin shugaban Biyu a fadar Janar Abdurahaman Bello Dambazau da ke zaman ministan tsaron cikin gidan Tarrayar Najeriyar

Abun jira a gani dai na zaman tasiri na ziyarar ga batun tsaro da ma habbakar cinikin da a yanzu ya tsaya a tsakanin alúmma maimakon gwamnatoci na kasashen.

Sauti da bidiyo akan labarin