1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon babin dangatakar EU da kasar Burma

January 6, 2012

Kungiyar Tarayyar Turai(EU) ta ce za ta bude ofishinta a Burma a matsayin bangare na sabon babin dangantaka tsakaninta da kasar da ke gudanar da sauye-sauye na siyasa

https://p.dw.com/p/13fX9
epa03022902 (FILE) A file picture dated 17 November 2011 shows Myanmar President Thein Sein arriving at the Bali Nusa Dua Convention Center before the opening ceremony of the Association of South East Asian Nations (ASEAN) Summit in Nusa Dua, Bali, Indonesia. According to media reports on 03 December 2011, Sein has signed a law allowing peaceful demonstrations as long as permission is sought five days in advance. The government has also pushed through a fairly liberal labor law, providing the right to unionize and has freed more than 300 political prisoners. EPA/STEPHEN MORRISON *** Local Caption *** 00000403006037 +++(c) dpa - Bildfunk+++
Thein Sein, shugaban kasar BurmaHoto: picture-alliance/dpa

A matsayin martaninta ga gyare-gyaren siyasa da ke wakana a kasar Burma Kungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta bude ofishinta a Rangoon babban birnin wannan kasa. Kakakin Catherine Ashton, kantomar kungiyar kan manufofin ketare ya ce ofishin zai rinka gudanar da ayyukan taimako a baya ga taka rawa a fannin siyasa. To amma kakakin ya ce ofishin ba shi da wakilici a hukumance. Bayan ganawarsa da shugaban adawar kasar, Aung San Suu Kyi a birnin Rangoon minstan harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya ce an fara ganin sauyin da ke wakana a gwamnatin mulkin sojin kasar ta Burma a kasa.To ama kuma ana bukatar yin matsin lamba ga gwamnatin farar hula da ke mulkin kasar. Hakazalika yayin ganawarsa da Shugaban Sein Thein, Hague ya sake yin kira da asaki dukkan firsinonin siyasa. A hukumance dai ita gwamnatin da aka girka a kasar ta Burma a watan Maris bara gwamnati ce ta farar da har yanzu ake damawa da tsoffin janar janar na soji da magoya bayan gwamnatin mulkin soji da dama a cikinta.

Mawalllafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Dan-Ladi Aliyu