Sabon babi a harkokin siyasar kasar Faransa | Labarai | DW | 11.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon babi a harkokin siyasar kasar Faransa

Jam´iyyar masu ra´ayin mazan jiya ta shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, ta samu nasarar lashe zaben yan majalisun dokokin kasar da aka gudanar da dan karamin rinjaye. Bayanai dai sun nunar da cewa jam´iyyar ta UMP da ragowar jam´iyyu da suke kawance da ita, sun samu kashi 45 daga cikin kuri´un da aka kada. Ita kuwa jam´iyyar adawa ta masu sassaucin ra´ayi da ragowar jam´iyyun da suke kawance da ita, sun samu kusan kashi 36 ne daga cikin dari. Za dai a tabbatar da sakamakon zaben ne a hukumance, bayan gudanar da zabe zagaye na biyu a mako mai zuwa. Kafafen yada labarai dai sun rawaito yan jam´iyyar ta UMP na cewa wannan nasara, zata bawa gwamnatin su damar cika alkawarurrukan da suka dauka, a lokacin yakin neman zabe. Gwamnatin dai ta Mr Sarkozy, tayi alkawarin rage haraji a kokarin inganta tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi.