1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabon adadi na cutar Kwalara a Haiti

Mutane 1,751 suka rasa rayukansu a cewar hukumomi ƙasar

default

Sabbabin alƙalluma da hukumomi suka bayyana a ƙasar Haiti sun nuna cewa Mutane 1,751 suka mutu a sakamakon cutar amai da gudawa ta kwalara. Alƙalluman wanda offishin ministan kiwon lafiya na ƙasar ya bayyana

Sun zo ne kwanaki biyu da gudanar da zaɓuɓɓukan 'yan Majalisun dokoki da aka yi ciki tashe-tashen hankula wanda a cikinsa mutane biyu suka rasa rayukansu.

Wanda kuma du da kura-kuran da aka samu hukumar zaɓen ta amince da sakamakon a mafi yawancin yankunan ƙasar , baya ga kashi ukku cikin ɗari na sakamakon mazaɓun da ta soke .

Suma dai wakilai na ƙungiyoin masu saka ido na Amurka da yanki Caraibien ba su amince ba a soke dukanin zaɓen kamar yadda wasu 'yan takara suka gabatar da bukatar tun can da farko.

Mawallafi:Abdurahamane Hassane

Edita : Zainab Mohammed Abubakar