Sabo saƙon Video daga Ayman al-Zawahiri | Labarai | DW | 05.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabo saƙon Video daga Ayman al-Zawahiri

Babban na hannun daman Osama bin Laden Ayman al-Zawahiri ya fidda wani sabon saƙo na Video inda yake kiran kai hare hare a kan cibiyoyi da kadarori mallakar yammacin turai a ko ina a faɗin duniya, tare kuma da kawo sauyin gwamnati a ƙasashen Masar da Saudiyya. Zawahiri wanda yayi kakkausar suka ga yammacin turai, yace labudda dukkan waɗanda suka kaiwa ƙasashen musulmi hari za su ɗanɗana kuɗar, su yana mai nuni da halin da ake ciki ƙasashen Iraqi da Afghanistan da yankin Palasɗinu da kuma Somalia. Wannan dai shine sako na takwas da zawahiri ya fitar a cikin wannan shekarar. A sakon na baya bayan nan Zawahiri yace domin cimma manufar da suka sanya a gaba, akwai buƙatar samun haɗin kan alúma ga wanzuwar jihadin Islama.