1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabiya ta nemi ahuwan kisan da akayiwa Musulman Bosniya 8000

March 31, 2010

Majalisar Dokokin Sabiya ta kaɗa ƙuri'ar neman gafaran kisan gillar da Sojojin Serbiyan sukayiwa Musulman Bosniya su 8000 a shekarar 1995

https://p.dw.com/p/MjJO
Majalisar Dokokin SabiyaHoto: AP Photo

Majalisar Dokokin Sabiya ta kaɗa ƙuri'ar neman gafaran kisan gillar da Sojojin Serbiyan sukayiwa Musulman Bosniya dubu 8000 a shekarar 1995 a Sebiraniska. Ƙudirin wanda 'yan majalisar dokokin 127 daga cikin 250 suka kaɗa kuri'ar amincewa dashi, yakawa ƙarshen musanta zargin kisa gillar da ake zargin Sabiyawan sun aikata akan musulman na Bosniya, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya tace kisan na ƙare dangi ne.

Yanzu haka dai al'uman musulman da kisan ya shafa sunyi Allah wadai da matakin 'yan majalisar, bisa ƙin bayyana kashe-kashen a matsayin kisan ƙare dangi.

Wannan mataki da majalisar Dokokin Sabiyan ta ɗauka na ɗaya daga cikin shirye-shiryen da takeyi na shigar da ita cikin ƙungiyar Tarayyar Turai. Haryanzu dai Kotun Duniya tana neman wani tsohon kwamandan Sojin na Sabiya da ake zargin ya jagoranci kisan domin fuskantar Shari'a.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed