Sabbin tashe tashen hankula a Sri Lanka | Labarai | DW | 15.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin tashe tashen hankula a Sri Lanka

Akalla sojojin gwamnati 4 suka kwanta dama sannan wasu suka samu raunuka a wani harin bam da ake zargin ´yan tawayen Tamil Tigers da kaiwa a arewacin kasar Sri Lanka. Kamar yadda rundunar soji ta nunar an dana bam din ne a daidai lokacin da wata safa dauke da sojoji ta zo wucewa. Da farko ´yan tawayen kungiyar Tamil Tigers ta ba da sanarwar janyewa daga tattaunawa samar da zaman lafiya a Sri Lanka. Babban mai shiga tsakani S. Puleedevan ya ce ´yan tawayen sun dauki wannan mataki ne don mayar da martani ga shirin gwamnati na sa ido akan wani jirgin ruwa, wanda zai yi jigilar shugabannin ´yan tawayen zuwa gun taron. Da farko dai an shirya ci-gaba da tattaunawar a birnin Geneva a ranar 24 ga watannan na afrilu.