Sabbin tashe tashen hankula a Somalia | Labarai | DW | 21.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin tashe tashen hankula a Somalia

An ba da rahoton barkewar wani kazamin fada tsakanin dakarun gwamnatin Somalia da sojojin sa kai na magoya bayan ´yan Islama a garin Bur Hakaba dake tsakiyar kasar. Bur Hakaba dai na tsakanin biranen Mogadishu da Baidoa mazaunin gwamnatin wucin gadin Somalia da ta yi rauni. Gwamnatin wadda kasar Habasha ke marawa baya, tana kara fuskantar barazana daga sojojin sa kai na Islama wadanda suka karbe ikon babban birnin kasar Mogadishu cikin watan yuni bayan an shafe watanni da dama ana bata-kashi, kuma yanzu haka suke iko da daukacin yankunan kudu da tsakiyar kasar ta Somalia.