Sabbin tashe tashen hankula a Iraki | Labarai | DW | 18.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabbin tashe tashen hankula a Iraki

Akalla mutane 17 sun rasu sakamakon sabbin hare hare da aka kai cikin Iraqi. Rahotanni sun ce jami´an tsaron kasa kimanin 11 na daga cikin wadanda aka bindige har lahira ko kuma hare-haren bama-baman suka yi sanadiyar mutuwar su a jerin tashe tashen hankula a Bagadaza da kuma yankin arewacin Iraqi. Sauran mutanen da tashe tashen hankulan na yau lahadi suka rutsa da su har da ´yan siyasa musamman na mabiya darikar shi´at da wata mace wadda ta gamu da ajalinta a tashin bam a kusa da wani masallacin ´yan shi´a da ke babban birnin na Iraqi. A halin da ake ciki shugabannin ´yan sunni da shi´a sun yi kira da a kwantar da hankali kuma a guji ta da zaune tsaye bayan zaben ´yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar alhamis da ta gabata.